Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 3:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙidaya dukan 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, tun daga wata ɗaya zuwa mai gaba, ka rubuta sunayensu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ƙidaya dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa maza daga wata ɗaya da kuma fiye ka kuma rubuta sunayensu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 3:40
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ya ƙidaya mazaje na kabilar Lawi bisa ga gidajen kakanninsu da iyalansu, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba.


Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,


Duk wanda ya ci nasara, za a sa masa fararen tufafi, ba kuwa zan soke sunansa daga Littafin Rai ba, zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, da kuma a gaban mala'ikunsa.


Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.


Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”


Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.


Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”


Duk wanda aka rage a Urushalima, wanda Ubangiji ya nufa da rayuwa, za a ce da shi mai tsarki.


Ubangiji zai rubuta lissafin jama'o'i, Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima.


“Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.


“Ga shi, na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa a maimakon kowane ɗan farin da ya buɗe mahaifa daga cikin mutanen Isra'ila. Lawiyawa za su zama nawa.


Za ka keɓe mini Lawiyawa a maimakon 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa za su zama nawa a maimakon dukan 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Ni ne Ubangiji.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ