Ƙidaya 3:38 - Littafi Mai Tsarki38 Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202038 Musa da Haruna da ’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ƙungiyoyin kabilar Yahuza za su sauka su kafa tutarsu a sashin gabas a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Yahuza Nashon ɗan Amminadab 74,600 Issaka Netanel ɗan Zuwar 54,400 Zabaluna Eliyab ɗan Helon 57,400 Jimilla duka 186,400 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza su ne za su fara tafiya.