Amma Lawiyawa za su sauka kewaye da alfarwa ta sujada don su yi tsaronta, domin kada wani dabam ya matsa kusa har ya sa in yi fushi in bugi jama'ar Isra'ila.”
Sa'an nan Lawiyawa ɗauke da alfarwa ta sujada za su kasance a tsakanin ƙungiyoyi biyu na farko da biyun da suke daga ƙarshe. Kowace ƙungiya za ta yi tafiya kamar yadda aka dokace ta ta zauna a zango, wato kowacce ta yi tafiya a ƙarƙashin tutarta a matsayinta.