Dukan Lawiyawa waɗanda Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga iyalansu, bisa ga umarnin Ubangiji, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mazaje dubu ashirin da dubu biyu ne (22,000).
Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci.
Haruna ne da 'ya'yansa maza za su nuna wa 'ya'yan Gershonawa irin aikin da za su yi, da kayayyakin da za su ɗauka. Sai a faɗa musu dukan abin da za su yi, da dukan abinda za su ɗauka.