Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 3:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Gama 'yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra'ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 gama duk ’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk ’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 3:13
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

(kamar dai yadda yake a rubuce a Shari'ar Ubangiji cewa, “Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce da shi tsattsarka ne Ubangiji”),


sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Kowane ɗan farin dabbarku na Ubangiji ne.


“Keɓe mini 'ya'yan fari maza duka. Kowane ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa cikin Isra'ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”


Kowane ɗan fari na dabba na Ubangiji ne, kada wani ya fanshi sa ko tunkiya, gama na Ubangiji ne.


Gama sa'ad da Fir'auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan 'ya'yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da 'ya'yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan 'ya'yan farinmu, maza.’


Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.


Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku.


“Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.


“Kowane ɗan farin mutum, ko na dabba nawa ne, duk da 'ya'yan farin dabbobinku, wato ɗan farin saniya da na tunkiya.


“Kada ku yi jinkirin fitar da zakar amfanin gonarku ta hatsi da ta abin matsewa. “'Ya'yan farinku, maza, kuma za ku ba ni su.


“Za mu kuma kawo 'ya'yan farinmu maza, da na shanunmu, da na tumaki, da awaki, kamar dai yadda aka rubuta a dokoki, haka za mu kawo su a Haikalin Allahnmu, da gaban firistocin da suke hidima a Haikalin Allahnmu.


Za ka keɓe mini Lawiyawa a maimakon 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa za su zama nawa a maimakon dukan 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Ni ne Ubangiji.”


Ga shi, ni na ɗauki 'yan'uwanku, Lawiyawa, daga cikin mutanen Isra'ila. Kyauta suke a gare ku, waɗanda aka bayar ga Ubangiji don su lura da alfarwa ta sujada.


Masarawa suna ta binne gawawwakin 'ya'yan farinsu da Ubangiji ya karkashe musu. Banda 'ya'yan farinsu kuma Ubangiji ya hukunta wa allolinsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ