Ƙidaya 29:6 - Littafi Mai Tsarki6 Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka'idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |