A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.
Kowace rana, tun daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra yakan karanta musu daga cikin littafin dokokin Allah. Suka kiyaye idin har kwana bakwai. A rana ta takwas kuma suka muhimmin taro bisa ga ka'ida.
A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai.