Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta lallausan gāri wanda aka kwaɓa da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da kowane rago,
Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.