Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da ragon,
Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, banda hadaya don zunubi saboda yin kafara, da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha.