Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 28:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Hadaya ce ta ƙonawa kullum, wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 28:6
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu,


Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum.


Ban tsauta muku saboda hadayunku ba, Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.


Suka kuma kiyaye Idin Bukkoki kamar yadda aka rubuta, suna miƙa hadayu na ƙonawa kowace rana bisa ga yawan adadin hadayun da ake bukata.


Daga dukiyarsa kuma ya ba da taimako na abin yin hadayun ƙonawa, wato hadayun ƙonawa na safe da na maraice, da hadayun ƙonawa na ranakun Asabar, da na amaryar wata, da na ƙayyadaddun idodi, kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Ubangiji.


Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.


ya ba Haruna da 'ya'yansa maza ka'idodin hadayu na ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za ta kwana bisa bagaden, wutar bagaden kuma ta kwana tana ci har safe.


Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.


Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba'in da dare arba'in.


Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.


da kuma mudun lallausan gari, kwaɓaɓɓe da man zaitun mafi kyau har rubu'in moɗa.


Hadaya ta sha za ta zama rubu'in moɗa na ruwan inabi domin kowane ɗan rago. Za a kwarara hadaya ta sha mai gafi ga Ubangiji a bagade.


Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.


Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra'ilawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ