A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka.
Kowace safiya da maraice suna miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a bisa bagaden ƙona hadaya, kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, waɗanda ya ba Isra'ilawa.
Ya ku firistoci masu miƙa hadayu a bagaden Ubangiji, Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka! Ku shiga Haikali, ku kwana, Kuna saye da tufafin makoki, Gama ba hatsi ko ruwan inabi da za a yi hadaya da su, A cikin Haikalin Allahnku.