Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.
Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.
Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”
idan jama'a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka'idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi.