Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 28:25 - Littafi Mai Tsarki

25 A rana ta bakwai za a yi tsattsarkan taro, ba za a yi aiki ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 28:25
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.


Za ku yi tsarkakakken taro a ranar fari ta idin, ba za a yi aiki ba.


Sai ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai, amma a rana ta bakwai za ku yi idi ga Ubangiji.


A kan rana ta fari za ku yi tsattsarkan taro, haka kuma za ku yi a rana ta bakwai. A cikin waɗannan ranaku ba za a yi kowane aiki ba, sai na abin da kowa zai ci.


A rana ta takwas za a taru domin yin sujada. Ba za a yi aiki ba.


A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai.


A rana ta fari ga wata na bakwai za a taru domin yin sujada, ba za a yi aiki a ranar ba. A ranar za a busa ƙahoni.


Za a yi tsattsarkan taro a ranar nunan fari, wato idi na mako bakwai lokacin da za a miƙa wa Ubangiji hadaya da sabon hatsi. A ranar ba za a yi aiki ba.


Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.


A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.


Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce.


Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba.


Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ