23 Za a miƙa waɗannan hadayu banda hadaya ta ƙonawa wadda akan miƙa kowace safiya.
23 Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya.
Waɗannan su ne hadayu na abinci da za a miƙa wa Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, raguna biyu 'yan bana ɗaya ɗaya marasa lahani.
Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace ranar Asabar, banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadaya ta sha.
Haka za a miƙa abinci na hadaya ta ƙonawa kowace rana har kwana bakwai, domin daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Za a kuma riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta sha.