21 gari humushi ɗaya tare da kowane ɗan rago.
21 da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
Za a kuma miƙa hadaya ta gari tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da man zaitun, gari humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gari humushi biyu tare da kowane rago,
Za a miƙa bunsuru guda don yin hadaya don zunubi, domin yin kafara.