Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 28:15 - Littafi Mai Tsarki

15 A kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi ga Ubangiji tare da hadaya ta ƙonawa, da hadayarta ta sha.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadaya ta sha, za a miƙa bunsuru ɗaya ga Ubangiji, hadaya ce don zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 28:15
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan su ne hadayu na abinci da za a miƙa wa Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, raguna biyu 'yan bana ɗaya ɗaya marasa lahani.


Za a miƙa bunsuru guda don yin hadaya don zunubi, domin yin kafara.


idan jama'a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka'idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.


Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.


Idan aka sanar da shi zunubin da ya yi, sai ya kawo bunsuru marar lahani don yin hadaya.


Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin.


Hadaya ta sha kuwa za ta zama rabin moɗa na ruwan inabi don kowane bijimi, sulusin moɗa kuma don kowane rago, rubu'in moɗa don kowane ɗan rago. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane wata na shekara.


Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra'ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu.


Za a miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi, domin a yi kafara.


Sai kuma a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi domin a yi kafara.


Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ