Ƙidaya 28:11 - Littafi Mai Tsarki11 A farkon kowane wata sai a miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da kuma 'yan raguna bakwai bana daya daya; marasa lahani, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 “ ‘A rana ta fari ga kowane wata, za a miƙa wa Ubangiji hadayun ’yan bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan tumaki bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu kuma marasa lahani. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.