Ƙidaya 28:10 - Littafi Mai Tsarki10 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace ranar Asabar, banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadaya ta sha. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace Asabbaci, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da ta hadaya ta sha. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.