Don me za a tsame sunan mahaifinmu daga cikin zuriyar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? In ka yarda, muna roƙonka ka ba mu gādo tare da 'yan'uwan mahaifinmu.”
Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”
Suka ce, “Ubangiji ya umarce ka ka raba wa Isra'ilawa gādon ƙasar ta hanyar jefa kuri'a. Ubangiji kuwa ya umarce ka ka ba 'ya'ya mata na Zelofehad, ɗan'uwanmu, gādo.
Suka zo wurin Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da 'yan'uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji.