Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra'ilawa dukansu suka yi masa biyayya.
Sa'ad da annabawa hamsin da suke Yariko suka ga ya haye ya nufo su, sai suka ce, “Ai, ruhun Iliya yana kan Elisha.” Sai suka tafi su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa,
Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.
Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”