Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 27:17 - Littafi Mai Tsarki

17 mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama'ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 yă shiga, yă kuma fita a gabansu, wanda zai bishe su zuwa waje, yă kuma dawo da su ciki, don kada mutanen Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyayi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 27:17
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai suka warwatsu saboda rashin makiyayin kirki, suka zama abincin namomin jeji.


Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.


Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”


Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi.


Gama maganar shirme kan gida yake yi, Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya, Masu mafarkai suna faɗar ƙarya, Ta'aziyyarsu ta banza ce. Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki, Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.


Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”


Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’


Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.


Saboda haka Saul bai yarda Dawuda ya zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban dubu. Shi kuwa ya riƙa bi da su cikin kai da kawowa.


don mu ma mu zama kamar sauran ƙasashe, mu sami sarki wanda zai sarauce mu, ya shugabance mu zuwa yaƙe-yaƙe.”


A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.


Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.


Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.”


Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila, Irm


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Mikaiya kuwa ya ce, “Ina ganin dukan Isra'ilawa a warwatse bisa tsaunuka, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Ubangiji kuma ya ce, ‘Waɗannan ba su da makiyayi, bari dukansu, kowa ya koma gidansa da salama.’ ”


A dā sa'ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra'ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, ‘Kai za ka lura da jama'ata Isra'ila, za ka zama sarkinsu.’ ”


Za ku kewaye sarki, kowane mutum ya riƙe makaminsa. Duk wanda ya yi ƙoƙari ya zo kusa, sai a kashe shi. Sai ku kasance tare da sarki duk lokacin da zai fita da duk lokacin da zai shiga.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ