8 Fallu ya haifi Eliyab.
8 Ɗan Fallu kuwa shi ne Eliyab,
'Ya'yan Ra'ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
Waɗannan yawansu ya kai dubu arba'in da uku da ɗari bakwai da talatin (43,730).
'Ya'yan Eliyab, maza su ne Yemuwel, da Datan, da Abiram. Datan da Abiram ne aka zaɓa daga cikin taron jama'ar, suna cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Musa da Haruna, har ma da Ubangiji.