Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 26:65 - Littafi Mai Tsarki

65 Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

65 Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 26:65
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai dai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne, kaɗai ne ba za su mutu ba daga cikin waɗanda suka tafi leƙen asirin ƙasar.


Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka.


Ni Ubangiji na faɗa, hakika, haka zan yi da wannan mugun taron jama'ar da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su ƙare ƙaƙaf a wannan jeji, a nan za su mutu.’ ”


Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.


Isra'ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot.


Amma ku, gawawwakinku za su fāɗi a jejin.


“Mahaifinmu ya rasu cikin jeji. Ba ya cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Ubangiji. Ya rasu saboda alhakin zunubinsa. Ga shi, ba shi da 'ya'ya maza.


Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza.


sai dai Kalibu ɗan Yefunne, shi kaɗai ne zai gan ta. Zan ba shi da 'ya'yansa ƙasar da ƙafarsa ta taka, gama shi ne ya bi Ubangiji sosai.’


Dalilin da ya sa Joshuwa ya yi musu kaciya ke nan, domin dukan waɗanda aka haifa a hanya cikin jeji bayan fitowarsu daga Masar, ba a yi musu kaciya ba. Dukan mazajen da suka fito daga Masar waɗanda suka isa yaƙi sun rasu cikin jeji a hanyarsu. Waɗannan kuwa an yi musu kaciya kafin fitowarsu.


Waɗanda suka dogara ga Ubangiji, Za su yi zamansu lafiya a ƙasar, Amma za a kori mugaye.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ