Waɗannan su ne karkasuwar gādon da Isra'ilawa suka karɓa a ƙasar Kan'ana, wanda Ele'azara, firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin iyalan kabilan Isra'ila suka ba su.
Haka nan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.
Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai na Ɗan Ragon kaɗai.
Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’
Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da suke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi 'ya'ya a cikinku. Za su zama kamar 'ya'yan Isra'ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra'ila,
Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki, Mutuwa ce za ta yi kiwonsu. Da safe adalai za su ci nasara a kansu, Sa'ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu, Nesa da gidajensu.
Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.