Yanzu fa, a kan waɗannan 'ya'yanka maza biyu da aka haifa a Masar kafin zuwana, su nawa ne, Ifraimu da Manassa za su zama nawa, kamar yadda su Ra'ubainu da Saminu suke.
Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, Da alherin wanda yake zaune a jeji. Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu, A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin 'yan'uwansa.
Jama'ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu.