9 Duk da haka annobar ta kashe mutane dubu ashirin da dubu huɗu (24,000).
9 Waɗanda suka mutu a wannan annoba, sun kai mutum 24,000.
Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak.
Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal'amu, suka yaudari Isra'ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama'ar Ubangiji.
mutanen nan da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta kashe su a gaban Ubangiji.
Ya kuwa tsaya a tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
Bayan annobar, sai Ubangiji ya ce wa Musa da Ele'azara, ɗan Haruna, firist,
Sai Ubangiji ya aika wa mutanen da annoba saboda ɗan maraƙin da suka sa Haruna ya yi musu.
Ubangiji kuwa ya aika da annoba a kan Isra'ila tun da safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade. Mutum dubu saba'in (70,000) suka mutu daga Dan zuwa Biyer-sheba.