Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 25:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ya bi Ba'isra'ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba'isra'ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra'ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 25:8
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ba ni wannan masussuka don in gina wa Ubangiji bagade. Ka sayar mini da masussukar a bakin cikakken kuɗinta, domin a kawar wa jama'a da annobar.”


Sa'an nan ya gina wa Ubangiji bagade a wurin. Ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama. Sa'an nan Ubangiji ya amsa masa addu'o'i saboda ƙasar. Aka kawar wa Isra'ila da annobar.


“Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra'ilawa saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka ban shafe Isra'ilawa saboda kishina ba.


Musa kuwa ya ce wa alƙalan Isra'ilawa, “Kowa ya kashe mutanensa da suka shiga bautar gumakan Ba'al-feyor.”


“Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai.


Duk wanda ya kusaci alfarwa ta sujada ta Ubangiji, zai mutu. Ashe, dukanmu za mu mutu ke nan!”


Suka tara tsibin duwatsu a kansu. Tsibin duwatsun kuwa yana nan har wa yau. Sa'an nan Ubangiji ya huce daga zafin fushinsa. Domin haka ana kiran wurin Kwarin Akor, wato azaba, har wa yau.


Aka binne ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan a kabarin Kish, tsohon Saul, a Zela a ƙasar Biliyaminu. Aka aikata dukan abin da sarki ya umarta. Bayan haka Allah ya ji addu'arsu a kan ƙasar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ