A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”
Duwatsu da tuddai za su ragargaje, Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam. Zan cika alkawarina na salama har abada.” Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.
Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”
“Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.