25 Sai Bal'amu ya tashi ya koma garinsu, Balak kuma ya yi tafiyarsa.
25 Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.
Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor.
Jama'ar Isra'ila kuma suka kashe Bal'amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi.
Yanzu sai ka tafi abinka. Hakika, na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi, Ubangiji ya hana maka ɗaukakar.”
Bal'amu ya ce wa Balak, “Yanzu fa, zan koma wurin mutanena. Ka zo in sanar maka da abinda mutanen nan za su yi wa mutanenka nan gaba.”
Sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango a Shittim, maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa.