Shi kuwa zai tashi ya ciyar da garkensa da ƙarfin Ubangiji, Da ɗaukakar sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuwa zauna lafiya, Gama zai zama mai girma cikin duniya duka.
Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.