39 Sai Bal'amu ya tafi tare da Balak suka je Kiriyat-huzot.
39 Sa’an nan Bala’am ya tafi tare da Balak zuwa Kiriyat-Huzot,
Bal'amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.”
Can Balak ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bal'amu da dattawan da suke tare da shi.
Mutanen Mowab sun gajiyar da kansu da zuwa wurin matsafarsu na kan dutse da masujadarsu, suna addu'a, amma ba zai amfana musu kome ba.