2 Balak ɗan Ziffor ya ga abin da Isra'ilawa suka yi wa Amoriyawa.
2 To, fa, Balak ɗan Ziffor ya ga duk abin da Isra’ila suka yi da Amoriyawa.
Kana zaton ka fi Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab? Ka ji ya taɓa hamayya da Isra'ilawa? Ko kuwa ka ji ya taɓa yin yaƙi da su?
Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.
Haka kuma Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya tashi ya yi yaƙi da Isra'ila, har ya gayyaci Bal'amu, ɗan Beyor, ya zo ya la'anta ku.