15 Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā.
15 Sai Balak ya aika waɗansu dattawa masu yawa, masu daraja kuma fiye da na dā.
Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal'amu bai yarda ya biyo mu ba.”
Suka je wurin Bal'amu, suka ce masa, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, ‘Kada ka bar wani abu ya hana ka zuwa wurina,