Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 21:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 21:5
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka yi magana gāba da Allah, suka ce, “Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada?


Kashegari dukan taron Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama'ar Ubangiji.”


Isra'ilawa suka ce wa Musa, “Ba shakka, mun hallaka. Mun lalace, dukanmu mun lalace.


Suka ce wa Musa, “Donin ba makabarta a Masar, shi ya sa ka fito da mu, mu mutu a jeji? Me ke nan ka yi mana da ka fito da mu daga Masar?


Wanda ya ƙoshi ba zai ko kula da zuma ba, amma wanda yake jin yunwa abinci mai ɗaci zaƙinsa yake ji.


Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki, Yakan fitar da 'yan sarƙa ya kai su 'yanci mai daɗi, Amma 'yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.


Isra'ilawa kuwa suka sa wa wannan abinci suna, Manna. Manna wata irin tsaba ce kamar farin riɗi. Ɗanɗanarta kuwa kamar waina ce da aka yi da zuma.


Sa'ad da Isra'ilawa suka gan shi, suka ce wa junansu, “Manna,” wato “Mece ce wannan?” Gama ba su san irinta ba. Musa kuwa ya ce musu, “Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci.


Sai mutanen suka yi wa Musa gunaguni suna cewa, “Me za mu sha?”


Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su.


“Amma 'ya'yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji.


Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa, suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ