Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 20:8 - Littafi Mai Tsarki

8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 20:8
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan.”


Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.


Har da namomin jeji za su girmama ni, Diloli da jiminai za su yi yabona Sa'ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada, Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena.


Sa'an nan, sai ya nuna mini kogin ruwan rai, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago,


Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu'a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.


Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”


To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”


Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.


Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi, Ba su sha wahalar ƙishi ba. Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu, Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.


Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa, Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai, Masu bulbulo da ruwa.


Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo, Yana gudu cikin hamada kamar kogi.


Da magana ya halicci duniya, Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.


Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa, Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi, Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.


Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, kowanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin.


Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.”


Rijiyar da hakimai suka haƙa, Shugabannin jama'a suka haƙa, Da sandan sarauta, Da kuma sandunansu.” Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.


da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”


Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Taron jama'a tare da garkunansu suka sha.


Sai Musa ya ce wa Joshuwa, “Zaɓo mana mutane, ka fita ka yi yaƙi da Amalekawa gobe. Zan tsaya a bisa dutsen da sandan mu'ujiza a hannuna.”


Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra'ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye.


Musa da Haruna kuwa suka yi daidai kamar yadda Ubangiji ya umarta. Sai Haruna ya ta da sandansa sama ya bugi ruwan Nilu a gaban Fir'auna da fādawansa. Dukan ruwan Nilu kuwa ya rikiɗe jini.


Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa.


Amma Ubangiji ya ce masa, “Mene ne wannan a hannunka?” Ya ce, “Sanda ne.”


Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ