Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 20:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Taron jama'a tare da garkunansu suka sha.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sai Musa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa. Ruwa kuwa ya yi ta kwararowa, jama’a da dabbobinsu suka sha.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 20:11
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.


Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.


Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.


“Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.”


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Ni ne wanda ya san ku a cikin jeji, A ƙasar da take da ƙarancin ruwan sama.


Ya sa rafi ya fito daga cikin dutse, Ya sa ruwan ya yi gudu kamar a kogi.


Gama Ubangiji Allahnmu ya fashe fushinsa a kanmu saboda ba ku ne kuka ɗauke shi a karo na farko ba, saboda kuma ba mu yi masa sujada kamar yadda aka umarta ba.”


Sa'an nan Saul ya ce wa Sama'ila, “Na yi zunubi, na yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da kuma koyarwarsa. Na ji tsoron mutanena, na kuwa biye wa abin da suke so.


Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.”


Me ya sa ba ka yi biyayya da shi ba? Don me ka fāɗa wason ganima, ka yi abin da Ubangiji ba ya so?”


'Ya'yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa kowannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.


Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu, Ka sa manyan koguna su ƙafe.


Ya tsaga duwatsu, suka buɗe a hamada, Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.


Gaskiya ce, ya bugi dutse, Ruwa kuwa ya fito a yalwace, Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama'arsa?”


Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo, Yana gudu cikin hamada kamar kogi.


Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa, Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai, Masu bulbulo da ruwa.


Ku duba abin da nake shirin yi. Yana ta faruwa ma, kuna iya ganinsa yanzu! Zan yi hanya a cikin jeji, In kuma ba ku rafuffukan ruwa a can.


Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi, Ba su sha wahalar ƙishi ba. Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu, Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.


Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ