Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 20:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sai dukan taron jama'ar Isra'ilawa suka zo jejin Zin a watan fari, suka sauka a Kadesh. A nan ne Maryamu ta rasu, a nan kuma aka binne ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A watan fari, dukan jama’ar Isra’ilawa suka iso Hamadan Zin. Suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta mutu, aka kuma bizne ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 20:1
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai suka haura, suka leƙo asirin ƙasar tun daga jejin Zin har zuwa Rehob kusa da Hamat.


Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh.


Sai Maryamu, annabiya, 'yar'uwar Haruna, ta ɗauki kuru cikin hannunta. Mata duka suka fita, suka bi ta da kuwaru suna ta rawa.


domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama'a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.)


wanda ya auri Yokabed 'yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yokabed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, 'yar'uwarsu.


Sai Maryamu da Haruna suka zargi Musa saboda mace, Bahabashiya, wadda ya aura.


Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu.


Muryarsa ta sa hamada ta girgiza, Ta girgiza hamadar Kadesh.


Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra'ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama'ar Isra'ila ba.


Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu.


Sa'ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala'ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka.


Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama'ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon.


Sa'ad da al'amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa.


'Yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?”


Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.


Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.


Sai taron jama'ar Isra'ila suka kama tafiya daga Kadesh, suka je Dutsen Hor, a kan iyakar ƙasar Edom. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna a can,


Kun kuwa zauna cikin Kadesh kwana da kwanaki, kamar dai yadda kuka yi.”


Amma sa'ad da suka baro Masar, sun bi ta jeji zuwa Bahar Maliya, suka zo Kadesh.


Sai suka juya suka je Enmishfat, wato Kadesh, suka kuwa cinye ƙasar Amalekawa da kuma ta Amoriyawa waɗanda suka zauna cikin Hazazontamar.


Sai Musa ya tuɓe wa Haruna rigunansa na firist ya sa wa Ele'azara ɗan Haruna. Haruna kuwa ya rasu a kan dutsen. Sa'an nan Musa da Ele'azara suka sauko daga kan dutsen.


“A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ