Firist kuwa ya umarta a fitar da dukan abin da yake cikin gidan kafin ya tafi ya dudduba tabo, domin kada kome da yake cikin gidan ya ƙazantu. Bayan haka sai firist ya shiga, ya duba gidan.
Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa'an nan zai tsarkaka.