A cikinku duk wanda ya kashe mutum ko ya taɓa gawa, sai ya zauna a bayan zango kwana bakwai don ya tsarkake kansa tare da bayin a rana ta uku da ta bakwai.
ya faɗa wa Isra'ilawa ya ce, “Idan wani mutum na cikinku, ko na cikin zuriyarku, ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji.
Akwai waɗansu mutane da suka ƙazantu ta wurin taɓa gawar wani mutum, don haka ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a ranar ba. Sai suka zo wurin Musa da Haruna a ranar,
balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.
To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi.
Sai kuma Haggai ya ce, “Idan wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, wannan zai sa abin ya ƙazantu?” Sai firistoci suka ce, “Wannan zai sa abin ya ƙazantu!”
Sa'an nan Bulus ya ɗibi mutanen nan, kashegari kuma da suka tsarkaka tare, sai ya shiga Haikali domin ya sanar da ranar cikar tsarkakewar tasu, wato ranar da za a ba da sadaka saboda kowannensu.
Ko kuma idan mutum ya taɓa kowane abin da yake haram ko mushen haramtacciyar dabba ta jeji ko ta gida, ko mushen haramtaccen abin da yake rarrafe, zai zama da laifi, ko da bai sani ba.
Ku fita, ku bar Babila Ku dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji! Kada ku taɓa abin da aka hana, Ku kiyaye kanku da tsarki, Ku fita ku bar birnin.
“Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,