Gama ni Ubangiji na ba su zaka da Isra'ilawa suke kawo mini ta hadaya ta ɗagawa ta zama gādonsu. Saboda haka ne, na ce ba su da gādo tare da Isra'ilawa.”
“Har yanzu ka faɗa wa Lawiyawa, cewa sa'ad da suka karɓi zaka daga Isra'ilawa wadda na ba su gādo, sai su fitar da zaka daga cikin zakar, su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa.