Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 18:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Gama ni Ubangiji na ba su zaka da Isra'ilawa suke kawo mini ta hadaya ta ɗagawa ta zama gādonsu. Saboda haka ne, na ce ba su da gādo tare da Isra'ilawa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 18:24
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Har yanzu ka faɗa wa Lawiyawa, cewa sa'ad da suka karɓi zaka daga Isra'ilawa wadda na ba su gādo, sai su fitar da zaka daga cikin zakar, su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa.


Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra'ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.


Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da 'yan'uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)


“Sa'ad da kuka gama fitar da zakarku ta amfanin gona a shekara ta uku, wadda take shekara ta fid da zaka, sai ku ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu, don su ci, su ƙoshi a cikin garuruwanku.


Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na 'ya'yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji.


Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.


Firist kuwa daga zuriyar Haruna zai kasance tare da Lawiyawa sa'ad da suke karɓar zakar. Lawiyawa kuma za su fid da zaka daga cikin zakar da aka tara musu, su kawo ɗakin ajiya na Haikalin Allah.


Sai dukan mutanen Yahuza suka kawo zakar hatsi, da ta ruwan inabi, da ta mai, a ɗakunan ajiya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ