Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 18:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Nunan fari na dukan amfanin gonarsu wanda suke kawowa ga Ubangiji, zai zama naka. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya cinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 18:13
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Kada ku yi jinkirin fitar da zakar amfanin gonarku ta hatsi da ta abin matsewa. “'Ya'yan farinku, maza, kuma za ku ba ni su.


Tawa ta ƙare, gama na zama kamar lokacin da aka gama tattara amfanin gona, Kamar lokacin da aka gama kalar 'ya'yan inabi, Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci, Ba kuma 'ya'yan ɓaure da suka harba wanda raina yake so.


Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi, Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure, Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al. Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.


A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu.


“Wajibi ne ku kawo mafi kyau daga cikin nunan fari na amfanin gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa.”


“Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”


to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa.


Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku.


To, sa'ad da rana ta faɗi mutumin zai tsarkaka, bayan wannan ya iya cin tsarkakakkun abubuwan nan, gama ko dā ma abincinsa ne.


Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa'an nan a toya. Hadaya ta 'ya'yan fari ke nan ga Ubangiji.


Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya.


Wani mutum ya zo daga Ba'alshalisha ya kawo wa annabi Elisha abinci na 'ya'yan fari, da dunƙule ashirin na sha'ir, da ɗanyun zangarkun hatsi. Sai Elisha ya ce wa baransa, ya ba ƙungiyar annabawa su ci,


Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko'ina, sai jama'ar Isra'ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ