Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 18:10 - Littafi Mai Tsarki

10 A wuri mai tsarki za ku ci shi, kowane namiji ya iya ci. Abu mai tsarki ne a gare ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ku ci shi a matsayin abu mafi tsarki; kowane namiji zai ci. Dole ku ɗauke shi da tsarki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 18:10
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne.


Kowane namiji a cikin firistoci zai iya cin naman, gama abu ne mafi tsarki.


Haruna da 'ya'yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada.


Amma zai iya ci daga cikin tsattsarkan abincin da aka miƙa mini, da abinci mafi tsarki.


Sa'an nan zai yanka ɗan rago a inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Tilas ya yi haka domin hadaya ta laifi rabon firist ne kamar hadaya domin zunubi. Hadaya ce mafi tsarki.


“Don me ba ku ci hadaya don zunubi a wuri mai tsarki ba, da yake tsattsarkan abu ne wanda aka ba ku domin ku kawar da laifin taron jama'a, domin kuma ku yi kafara dominsu a gaban Ubangiji?


Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni.


Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada.


Kowane ɗa namiji cikin 'ya'yan Haruna zai iya ci daga cikin hadayun Ubangiji waɗanda akan yi da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk wanda ya taɓa hadayu zai tsarkaka.


Abin da ya ragu daga cikin hadaya mafi tsarki da ake miƙa mini zai zama rabonka da na 'ya'yanka, wato daga kowace hadaya, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi.


“Har yanzu kuma duk sadakokin da Isra'ilawa suke bayarwa don hadaya ta ɗagawa da ta kaɗawa, na ba ka, kai da 'ya'yanka mata da maza, a kowane lokaci. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya ci.


Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ