Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi alfarwa ta sujada da su, yadda aka lasafta bisa ga umarnin Musa domin aikin Lawiyawa a ƙarƙashin jagorar Itamar, ɗan Haruna firist.
A maimakon haka, sai ka sa Lawiyawa su zama masu lura da alfarwa ta sujada da kayayyakinta. Za su ɗauki alfarwar da kayayyakinta, su yi aikinta, a zango kuma sai su sauka kewaye da ita.
Amma Lawiyawa za su sauka kewaye da alfarwa ta sujada don su yi tsaronta, domin kada wani dabam ya matsa kusa har ya sa in yi fushi in bugi jama'ar Isra'ila.”
Musa kuwa ya yi magana da Isra'ilawa. Sai dukan shugabanninsu suka ba shi sanda ɗaya ɗaya, sanda ɗaya daga kowane shugaba bisa ga gidajen kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Sandan Haruna yana cikin sandunan.