Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”
Kuna ganin wannan ƙaramar magana ce, wato cewa Allah na Isra'ila ya keɓe ku daga cikin jama'ar Isra'ila domin ya kawo ku kusa da shi, ku yi aiki a alfarwar sujada ta Ubangiji, ku kuma tsaya a gaban jama'a don ku yi musu aiki?