Sa'an nan ya gina wa Ubangiji bagade a wurin. Ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama. Sa'an nan Ubangiji ya amsa masa addu'o'i saboda ƙasar. Aka kawar wa Isra'ila da annobar.
Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.
Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa'an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna.
Sai Haruna ya ɗauko farantin turaren, ya yi yadda Musa ya ce. Ya sheƙa a guje a tsakiyar taron jama'a. Amma an riga an fara annobar a cikin jama'a. Sai ya zuba turare, ya yi kafara domin jama'a.