Sa'an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade.
Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”
Sa'ad da suke karkashewar, aka bar ni, ni kaɗai, sai na faɗi rubda ciki, na yi kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah za ka hallaka dukan sauran Isra'ilawa saboda zafin fushinka a kan Urushalima?”