Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 16:38 - Littafi Mai Tsarki

38 Waɗannan farantan ƙona turaren sun zama tsarkakakku sa'ad da aka miƙa su a bagaden Ubangiji. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo, musu mutuwa, ka ƙera murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, ta haka za su zama gargaɗi ga jama'ar Isra'ila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 gama an yi amfani da farantan don miƙa mini turare. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo musu mutuwa ka ƙera farantan, ka yi murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, suka zama tsarkakakku. Bari su zama alama ga Isra’ilawa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 16:38
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

da yake kuma ya mai da biranen Saduma da Gwamrata toka, ya yi musu hukuncin hallaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah,


Zan yi gāba da mutumin nan, zan sa ya zama abin nuni, da abin karin magana, in datse shi daga cikin mutanena, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.


Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.


Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora. Wuta kuma ta cinye sauran mutanen ƙungiyar, mutum ɗari biyu da hamsin suka mutu. Suka zama abin faɗakarwa.


Ka jawo wa gidanka kunya, Saboda ka karkashe mutane da yawa, Ka hallaka kanka da kanka.


Sai sarki Sulemanu ya rantse da Ubangiji ya ce, “Allah ya kashe ni nan take idan ban sa Adonija ya biya wannan roƙo da ransa ba.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Mayar da sandan Haruna a akwatin alkawari, alama ce ga masu tawaye ta cewa za su mutu idan ba su daina gunaguninsu ba.”


To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.


Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa, Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.”


Amma waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko. Ba za su kama kome ba, sai rayukansu.


Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.


“Ka faɗa wa Ele'azara, ɗan Haruna firist, ya kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, ka watsar da gawayin daga farantan a wani wuri gama farantan tsarkakakku ne.


Sai Ele'azara, firist, ya ɗauki farantan tagullar waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo. Aka ƙera murfin bagade da su.


“Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ