Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 16:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutane 250 da suke miƙa hadaya da turare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 16:35
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora. Wuta kuma ta cinye sauran mutanen ƙungiyar, mutum ɗari biyu da hamsin suka mutu. Suka zama abin faɗakarwa.


Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji.


Wuta ta sauko bisa magoya bayansu, Ta ƙone mugayen mutanen nan.


Sa'an nan kowane ɗayanku ya ɗauki farantinsa na ƙona turare, ya zuba turaren wuta a ciki, ya kawo a gaban Ubangiji, wato farantan ƙona turare guda ɗari biyu da hamsin ke nan. Kai kuma da Haruna kowannenku ya kawo nasa faranti.”


In kuwa wani yana da niyyar cutarsu, sai wuta ta huro daga bakinsu, ta lashe maƙiyansu, duk mai niyyar cutarsu kuwa, ta haka ne lalle za a kashe shi.


Sai Isra'ilawa duka waɗanda suke kewaye da su suka gudu saboda kururuwansu, suka ce. “Mu mā gudu, kada kuma ƙasa ta haɗiye mu.”


Waɗanda annoba ta kashe mutum dubu goma sha huɗu ne da ɗari bakwai (14,700), banda waɗanda suka mutu a sanadin Kora.


Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba, Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.


Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.


Amma Nadab da Abihu sun mutu a gaban Ubangiji a jejin Sinai, a sa'ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta. Sun mutu, ba su da 'ya'ya, saboda haka Ele'azara da Itamar suka yi aikin firist su kaɗai a zamanin mahaifinsu Haruna.


mutanen nan da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta kashe su a gaban Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ