Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 16:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Suka taru a gaban Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun cika izgili, gama dukan taron jama'a na Ubangiji ne, Ubangiji kuwa yana tare da su. Me ya sa kai Musa ka aza kanka shugaba a kan taron jama'ar Ubangiji?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 16:3
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Can cikin hamada suka ji kishin Musa Da Haruna, bayin Ubangiji, tsarkaka,


Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta.


za ku zama daular firistoci da al'umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne zantuttukan da za ka faɗa wa Isra'ilawa.”


Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”


“Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Mai Tsarki tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi.


Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciya tasu ta koma ƙasar Masar.


Daga Sinai da dubban manyan karusansa, Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.


Gama sun auro wa kansu da 'ya'yansu 'yan matan mutanen nan. Yanzu tsattsarkar zuriya ta cuɗanya da mutanen ƙasashe. Shugabanni da magabata sun fi kowa laifi kan wannan rashin gaskiya.”


Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, wadda ni kuma nake zaune a ciki, gama ni Ubangiji ina zaune a tsakiyar jama'ar Isra'ila.”


Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!”


Su fitar da mace ko namiji daga cikin zango, don kada su ƙazantar da zangonku inda nake zaune.”


Kashegari dukan taron Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama'ar Ubangiji.”


Bai ga mugunta ga Yakubu ba, Bai kuma ga wahala a Isra'ilawa ba. Ubangiji Allahnsu yana tare da su, Suna sowar murna domin shi sarkinsu ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ